Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp . Kasance tare da mu don samun rahotanni da Dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Saudiyya - Wata kotun ɗaukaka ƙara a Saudiyya ta tabbatar da hukuncin kisa kan Anojan Sivarasa, matashi ɗan kasad Sri Lanka mai shekara 24.
Kotun ta yanke masa wannan hukunci ne bayan an same shi da laifin yin ɓatanci ga addinin Musulunci da Annabi Muhammad SAW a wani saƙon da ya wallafa a kafar sada zumunta.
Shugaban Amurka ya ɗora laifin abin da ke faruwa a Faransa kan addinin Musulunci
BBC Hausa ta ruwaito cewa mahaifiyarsa, Rasamanickam Yogalakshmi, ta roƙi a yi wa ɗanta afuwa cikin kuka, Tana mai cewa: "Don Allah ku yafe masa, ku dawo mana da shi."
Zaɓi Legit.ng Hausa a matsayin kafar labarai ta farko, labaran da muke wallafawa za su riƙa fitowa a saman shafinka na Google!
Lamarin ya tayar da hankula a faɗin Sri Lanka, inda ƙungiyoyin farar hula suka gabatar da ƙorafi. Jam’iyyun siyasa da hukumomin gwamnati da dama sun haɗa kai Wajen ƙoƙarin ganin an yi masa afuwa.
Iyalin matshin sun ce har yanzu ba su samu wani ƙarin bayani kan halin da yake ciki ba tun ranar 28 ga Satumba, 2026, amma gwamnatin Sri Lanka ta kwantar masu da hankali.
Har yanzu dai Saudiyya ba ta sanar da ranar zartar da hukuncin kisa kan matashin ba yayin da kasar Sri Lanka ta ce tana kokarin warware lamarin ta hanyar diflomasiyya.
Dan majalisar tarayya da yi wa Obi shagube kan zabe ya sha ihun 'ba mu yi'
Bayanai sun nuna cewa an gurfanar da Anojan ne bayan wata takaddama da ta taso a shafukan sada zumunta sakamakon wani lamari da ya faru yayin wani aikin ibada na mabiya addin Hindu a Sri Lanka.
A ƙarshen watan Yuni, wani bidiyo da ke nuna wani matashi Musulmi yana dukan wani kare da ke bin mabiya addinin Hindu ya yaɗu sosai a shafukan sada zumunta.
Lamarin ya haifar da muhawarar addini a intanet. A yayin muhawarar, wani mai amfani da shafin ya yi kalaman ɓatanci ga wani abin bautar mabiya addinin Hindu.
Hakan ya sa Anojan ya Mayar da martani da harshen Tamil, inda yi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad SAW amma daga bisani ya gode, sai dai wasu sun riga sun dauki hoton abin da ya fada
Bayan haka ne aka kai batun ga kamfanin dayake yi wa aiki da kuma hukumomin Saudiyya, Lamarin da ya kai ga kama shi a watan Yulin da ya gabat, har aka yanke masa hukuncin kisa a watan Satumba.
අන් හුකුන්ට මවකියා කසාර් ඉරාන් කන් රාෂින් සකා හිජාබි යායින් වƙa
Kun ji cewa hukumomin tsaron Saudiyya sun kama mutane 14,782 da ake zargi da karya dokokin zama da shigowa kasar ba bisa ka'ida ba cikin mako guda.
Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar ta ce an gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro da hukumomin gwamnati tsakanin ranar 10 zuwa 16 ga Satumba, 2026.
Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin ෆාරියා ලෙගිටයි da dama na turanci da Hausa tun 2012. තැපෑල: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262
Loading comments…